Thursday, March 11, 2021

Home › › BANBANCI TSAKANIN COIN DA KUMA TOKEN*

 


*BANBANCI TSAKANIN COIN DA KUMA TOKEN* 

  Kamar yadda na fada a baya coins sune suke da tasu hanyar kididdige da kuma ajiye bayanai da kuma tsare su. 
Yayin da su kuma tokens suna dogara ne da wasu coins din.
  Misalan Coins sune : Bitcoin (BTC), Ethereum (ETH), Binance coin (BNB), Thunder Token (TT)  Tron (TRX) da dai sauran su.
 Misalan Tokens kuwa sune : 
- Bittorent (BTT) wanda aka Gina kan blockchain Na Tron.
- Smart key (SKY) Wanda aka Gina kan blockchain Na Ethereum.
- Trust wallet token (TWT) wanda aka Gina kan blockchain Na Binance.
 Da dai sauran su.
 
 *BANBANCI TSAKANIN ERC 20 , TRC 20 , BEP 2 DA KUMA BEP 20.* 

  *ERC20 :* Shine token din da aka Gina kan blockchain Na Ethereum.
 *TRC20 :* Shine Token din da aka Gina kan blockchain Na Tron.
 *BEP20 :* Shine token din da aka Gina kan blockchain Na Binance Smart chain. 
*BEP2 :* Shine token din da aka Gina kan blockchain na Binance coin *BNB* 

  *ABIN LURA :* 
A kullum ana kara cigaba ne, hakan yasa ake samun wasu abubuwan da babu su a baya. Daga cikin wadannan abubuwan akwai :
- Zuwan Tron da kuma Binance Coin Kasancewar Ethereum yana da charges da yawa wajen transfer hakan yasa wanda ya kirkiri Tron saukaka wannan matsalar Inda ya Samar da sauki wurin charges. Haka kuma Suma masu Binance coin sun saukaka sosai wurin transfer.
- Saurin transfer Ya karu fiye da yadda aka sani kan Ethereum domin kuwa transfer akan blockchain Na Tron da kuma Binance suna da matukar sauri idan aka hada da Na Ethereum.
No comments:
Write Comments