Wednesday, March 10, 2021

Home › › *MA'ANAR CRYPTO CURRENCY ?*







 *MENE NE CRYPTO CURRENCY ?* 

Crypto a turance Na nufin Abun da ke da tsaro.

  Crypto Currency ko kuma digital Currency a wani turancin yana nufin kudi amma Na kan internet.

 Kudade ne yadda ka San ko wane irin kudi amma su baa ganin su da ido (kamar yadda baka ganin kudin dake bankin)a kan internet suke kuma ana saye da sayarwa da su ana iya canja su (wato sayarwa) sa'annan su zama kudi tsaba.

Wani zai iya cewa wannan ai shirme ne 

Sai in ce : karamin misalin da zan iya baka shine : Yanda kake sa kudi a banki daga bisani su rikide su zama numbobi ko kuma a turo ma numbobin daga wani wuri kuma ka iya cire su  haka  Crypto Currency yake sai dai crypto currency yana da tsaron da banki basu da shi domin kuwa baa iya hacking nashi, shi yasa ma ake kiran su da crypto hakan na faruwa ne saboda amfani da amfani da ake yi da fasahar block chain.

 Irin wadannan kudaden suna da yawa sosai amma shahararru daga ciki sune Bitcoin(BTC) Ethereum (ETH)  XRP   Litcoin (LTC) Bitcoin Cash (BCH) Binance Coin (BNB) da dai sauran su.

 Wadannan kudaden suna da matukar daraja domin kuwa a yanzu haka Bitcoin daya ya kai kusan  Milyan 20 da wani abu. Yayinda Ethereum ya haura dubu 700.

No comments:
Write Comments