*MENE NE BLOCK CHAIN ?*
A takaice Block chain wata fasaha ce dake kididdige duk wani transaction din da ake yi da cypto currency (sending and receiving) sa'annan blockchain yana da tsaron da baa iya hacking nashi.
Bayan mutum yayi transaction wato ya tura kudi (crypto currency) wasu numbobi cakude da haruffa zasu wanzu domin zama shaida a lokacin da ake bukatar hakan idan ka danna kan wadannan haruffan/numbobin zasu kai ka kai tsaye zuwa ga bayanan da suka shafi wannan transfer ko bayan shekaru Nawa ne.
Misalin hash I'd kuwa shine : ```0x83b14227bf9a05d579cb6960f2db29a7c89f0314523377cd1e1bf2c5e4972efd```
Akwai currencies din da suna da nasu blockchain din kamar Bitcoin, Ethereum,Thunder Token, Tron , BNB, Ethereum classic, Tomo chain, Kin, XRP, Stellar da dai sauran su ana kiran su (COINS)
Akwai kuma wadanda basu da tasu hanyar kididdige da kuma ajiye bayanai ana kiransu da suna Tokens.



No comments:
Write Comments